<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><copyright>Public Domain</copyright>
<hymn_number>210</hymn_number>
<title>Sai Ku Nemi Shawara Gun Yesu Fa LW210</title>
<lyrics>[V1]
 1) Sai ku nemi shawara gun Yesu fa.
 Kome ya same ku nan a duniya,
 Sai ku shaida masa, ku ji nufinsa.
 Yesu ne mai shawararmu dai.

[V2]
 KORUS
 Yesu Kristi
 Shi zai taimake mu cikin dukan kome.
 Yesu Kristi
 Shi ne mai taimakon mu Masu Bi.

[V3]
 2) Ko mun fāɗa cikin tarkon jaraba,
 Sai mu nemi  ƙarfafawa wurinsa.
 Ko mun yi tuntuƃe har da faɗuwa,
 Sai mu nemi gafara tun yau.
 Korus

[V4]
 3) Ko mun fāɗa cikin ƙuncin tsanani,
 Sai mu nemi ƙarfi wurin Mai Ceto
 Muna so mu zama masu shaidarsa,
 Kada mu yi musun sunansa.
 Korus</lyrics>
<author>By R. Kelso Carter (1849-1926)</author>
</song>